Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban hukumar fansho ta jihar kano Alh. Habu Mohd fagge, ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda yan kame wuri zauna suka mamaye gidajen hukumar dake rukunin gidaje na Bandirawo da kuma wasu shaguna dake unguwar Panisau a dake karamar hukumar Ungoggo .
Alh. Habu Fagge ya baiyana damuwarsa ne kan gidajen a lokacin da ya kai ziyara ganin halin da gidajen suke a wannan rana ta Alhamis.
Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi
Shugaban hukumar ta Fansho Alh. Habu Mohd fagge ya ce gwamnatin jihar kano bisa jajoranci Engr. Abba Kabir Yusuf tayi Alwashi zata fito da hanyoyin kyautatawa duk wane dan fansho dake jihar nan.
” Ina kira ga duk wadanda suke cikin gidajen ‘yan fansho da sauran kadarorin yan fansho da su gaggauta fice daga cikin su , kafin gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace akan su, wanda kuma ba zai yiwa wadanda suke ciki dadi ba”. Inji Habu Muhammad Fagge
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya bayyana ranar da zai mikawa majalisa sunayen kwamishinonini
Hukumar Kuna ta kai ziyara kasuwar Sabon Gari inda hukumar take da shaguna akalla guda 52.
Yayin ziyarar shugaban hukumar yana tare da Sakataren hukumar Alh. Yahaya Nuhu Danbatta da dactan yada labarai na hukumar Umar Abdu kurmawa da dai sauransu.