Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar dokokin jihar Kano ta amincewa gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da nadin mukamai na musamman guda ashirin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin da yasa ta rushe shatale-talen gidan gwamnati
Jaridar kadaura24 ta ruwaito cewa an amince da amincewar ne a yayin wani zama da shugaban majalisar, Ismail Jibrin Falgore ya jagoranta kamar yadda sashi na 196/2 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada.
Hotuna: yadda Aka rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Majalisar, Uba Abdullahi ya fitar ta ce amincewar ta biyo bayan wasikar da Gwamnan ya aike wa majalisar na neman nadin wanda aka tattauna a gaban zauren majalisar tare da cimma matsaya.
Majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Yuni, 2023 a wani kudiri da shugaban masu rinjaye Hon Lawan Husaini na mazabar Dala ya gabatar kuma ya samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye Labaran Abdul Madari wakilin karamar hukumar Warawa.