Da dumi-dumi: Kwankwaso ya bayyana abubuwan da suka tattauna da Shugaba Tinubu

Date:

Daga Zakariyya Adam Jigirya

 

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ne ya gayyaci su, shi da tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan rushe-rushen da ake yi a jihar .

 

Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya ce Ganduje a matsayinsa na gwamna ya hana shi daga jihar Kano tsawon shekaru uku da rabi.

 

Da yake amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa, Kwankwaso ya yi ikirarin cewa yawancin gine-ginen da aka rushe gwamnatin Ganduje ce ta sayar da su, ba bisa ka’ida ba, kuma shugaban kasa Tinubu ya kadu a lokacin da ya yi masa bayanin hakikanin abin da yasa ake rushe gine-ginen a halin yanzu.

Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamnan CBN, Emefiele

Da aka tambaye shi ko ya gamsu da sanya bakin da shugaban kasa yayi akan rushe gine-ginen, sai ya ce: “Shugaban ya kadu Shin ba za ku yi mamakin ace muku wani ya sayar da Jami’a ba? Baku yi mamakin yadda ya rusa jami’a ba? Wato Daula Hotel, ga wadanda suka San Kano, ai kun san tsohur Daula, wadda aka aka rushe, to fa wata tsangaya ce a cikin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, shin abun bai baku mamaki ba?” Inji Kwankwaso

Da dumi-dumi: Da na sami Kwankwaso a fadar shugaban kasa da na dalla masa Mari –  Ganduje

“Shugaban kasar ya yi mamaki. Saboda bai sani ba. Ai lokacin Sallar idi ya karato da zaka yi Sallah a filin da kayi takaicin yadda aka mayar da wurin Sallah kasuwa.

 

Dangane da batun gidan jaridar triumph kuwa, Kwankwaso yace yan jarida dole su kasance cikin bakin cikin idan suka ga yadda akai da gidan jaridar ta yadda aka rushe shi aka mayar da wajen shagunan harkokin kasuwanc.

A cewar Kwankwaso, jam’iyyarsa a karkashin Gwamna Abba Yusuf, tana cika alkawuran yakin neman zabe ne kawai na rushe irin wadannan gine-gine.

Dangane da rade-radin karbar mukamin minista daga gwamnatin Tinubu, Kwankwaso ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar hakan.

Sai dai ya yi watsi da rade-radin sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki, inda ya jaddada cewa Tinubu ya fi mayar da hankali ne kan gwamnatin hadin kan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...