Ganduje ya bude gidan wutar lantarki mallakin kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bude sabon gidan wuta na tiga mallakin Kano, wanda zai samar da hasken wutar lantarki mai karfin mega wat goma.

 

A yayin da yake bude gidan wutar tare da wajen rarraba wutar lantarki dake Taburawa, Gwamna Ganduje yace an kashe Naira biliyan goma Sha hudu wajen samar da gidan wutar, wanda zai Rika baiwa fitulun kan titi da gidan ruwa da kamfanonin watar.

Yace sabon gidan wutar zai farfado da masana’antun da suka durkushe da kuma magance matsalolin rashin tsaro da ake samu da daddare saboda rashin haske har ma inganta tattalin arziki jihar kano.

KAYYASA! : Awanni kadan kafin saukarsa, Ganduje ya Rantsar da Sabon kwamishina

Kazalika gwamnan Ganduje ya bude sabon hotel din daula wanda gwamnatin ta sabuntashi tare da bude sabbin shagunan da gwamnatin ta gida a harabar tsohon gidan jarida na triumph Wanda gwamnan yace zasu samarwa gidan jaridar sama da naira miliyan arba’in a dukkan shekara.

” Gwamnatin mu ta Maida hankali wajen kulla aka da kamfanoni masu zaman kansu don inganta tattalin arzikin jihar da kuma magance wufuntar da kaddarorin gwamnatin jihar kano”. Inji Ganduje

A wannan rana da ya rage kasa da awanni 40 Ganduje ya sauka daga mulki jihar kano ya bude ginin Otel din Daula da ginin shagunan a tsohon ginin truimp

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...