Daga Abdulrashid B Imam
Zababben sanatan Kano ta Kudu, Sen Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila OFR, ya jagoranci mika gudunmawar shanu domin yankawa da yin liyafa ga jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma zababban gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, a wani bangare na shirin bikin rantsar da sabuwar gwamnati a jihar Kano.
Sanata Kawu ya jagoranci kungiyar mahauta ta santoriyar Kano ta Kudu, inda a madadin kungiyar ya mika gudunmawar shanu ga Sanata Kwankwaso.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman 2 kan kafafen yada labarai ga kawu Sumaila, Abbas Adam Abbas ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Ganduje ya bude gidan wutar lantarki mallakin kano
Mambobin kungiyar mahautan sun fito daga kananan hukumomi 16 na santoriyar Kano ta Kudu.
Shugaba Buhari zai yiwa yan Nigeria jawabin bankwana
Yayin mika shanun, Sanata Kawu ya shaidawa Kwankwaso cewar mahautan yankin Kano ta Kudu da ma sauran al’ummar yankin a shirye suke wajen ganin Zababben gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya samu nasara a gwamnatin sa.
A nasa bangaren, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya godewa Sanata Kawu da shugabancin kungiyar mahautan Kano ta Kudu, inda ya ba su tabbacin cewar Abba Gida-Gida zai yi aiki tukuru wajen ciyar da jihar Kano gaba.
Za a rantsar da sabon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a ranar Litinin 29 ga wannan wata na Mayu.