Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Shugaban kasa Muhammad Buhari zai gabatar da jawabin bankwana ga al’ummar Nigeria a gobe Lahadi, 28 ga watan mayu 2023 da misalin karfe 7 na safe a matsayin sa na shugaban kasar tarayyar Nigeria.
Kadaura24 ta rawaito mashawarci na musamman ga Shugaban kasar kan harkokin yada labarai Femi adeshina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da daddaren nan.
Ganduje ya bude gidan wutar lantarki mallakin kano
Sanarwar ta bukaci kafafen yada labarai na Tv da su jona jawabin daga gidan Talabishin na kasa NTA , yayin da su kuma gidajen Radio aka bukaci da su jona jawabin daga Gidan Radio tarayya FRCN.
Wannan jawabi dai shi ne zai zama jawabi na ƙarshe da Buharin zai yiwa yan Nigeria a matsayin Shugaban kasar Nigeria.