Daga Auwal Alhassan Kademi
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce bai sace dukiyar al’umma ba a tsawon shekaru takwas da yayi yana gwamnan jihar kaduna.
El-Rufai ya bayyana haka ne a karshen mako a lokacin da ya gudanar da taron manema labarai na karshe a matsayinsa na gwamna.
Kadaura24 ta ruwaito cewa El-Rufai zai mika wa zababben Gwamna Uba Sani, mulkin jihar nan da mako guda Mai zuwa.
“Zan iya rantse ban taba satar ko sisin kobo a cikin asusun gwamnati ba,” in ji Gwamna El-Rufai yayin da yake mayar da martani ga sukar da ake masa akan yadda ya rike mulkin jihar.
Mutane huɗu sun rasu a fashewar tukunyar gas a Sokoto
El-Rufai ya kara da cewa gida daya yake da shi kuma ya gina shi ne kafin ya zama gwamna, kuma shi zai koma idan ya sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
“Wadanda suke maganar sun ranto kudaden ya kamata su sani ba mu ranto kudaden don gudu zuwa Dubai don siyan gidaje ko mu je Jabi Road mu gina manya-manyan gidaje ba, kawai mun yi aiyukan Gina jihar mu kuma kowa ya gansu”. A cewar El-Rufai
“Na zama gwamnan Kaduna Ina da gida daya dake kan titin Danja a Ungwan Sarki. Yanzu ma dana gama gwamna shi ne dai yana nan ban Gina Wani ba, kuma bana bukata.
“Ban sack kudin kowa ba, kuma ina kalubalantar duk wadanda suka yi mulkin jihar nan da su fito su rantse da Alkur’ani cewa, a lokacin da suke mulkin jihar, ba su saci ko sisisn kobo na al’ummar jihar Kaduna ba.”