Shugabannin kasashe biyar ake sa ran za su bude matatar man Dangote

Date:

 

A yau Litinin ne 22 ga watan Mayu na 2O23 matatar man Dangote da ke jihar Lagos za ta fara aiiki.

 

Rahotanni sun nuna cewa matatar wadda za ta rinka tace gangar mai 650,000 a duk rana za ta rika samun danyen mai daga Afirka da Asia da kuma Amurka.

Haka kuma matatar kamar yadda rahotanni suka nuna za ta rika samar wa Najeriya kusan liti miliyan 38 ta fetur da man gas na dizil da kananzir da kuma man jirgin sama.

Hakan na nufin matatar wadda ke Ibeju-Lekki, a jihar ta Lagos za ta samar da kashi dari bisa dari na bukatar man Najeriya.

Haka kuma bayanai da jaridar Punch ta ruwaito sun nuna cewa, matatar ta Dangote za ta iya taimakawa wajen kafa gidajen sayar da mai 26,716 da samar da aikin yi ga mutane 100,000 da kuma samar da ciniki ga danyen man Najeriya har na dala bliyan 21 a shekara.

 

Ana sa ran shugabannin kasashe kusan biyar ne zasu harci taron bude matatar har kuma da zaɓaɓɓen shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu da mataimakin sa kashim Shattima da sauran manyan yan kasuwa daga sassa daban-daban na duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...