Kwanaki kadan ya mika mulki, wani gwamna ya amince da fitar da 2bn don a siyo masa sabbin motoci

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

A yayin da ya rage sauran ƴan kwanaki ya yi bakwana da kujerar mulki, gwamnan jihar Taraba ya amince da fitar da N2bn, domin a siyo masa sabbin motoci na kece raini.

Ba gwamnan ne kawai zai amfana da wannan garaɓasar ba, har da mataimakinsa da matansu, za a siyowa sabbin motocin.

Mutane 7 Sun Rasa Rayukansu Bayan Sun Sha Wani Shayi A Gidan Biki A Kano

Tuni har majalisar zartaswar jihar ta amince da fitar da kuɗin domin a siyo motocin.

Zamu kwace duk kadarorin gwamnati da Ganduje ya siyar – Dr. Baffa Bichi

“Gwamna Darius Ishaku a lokacin zaman mu na majalisar zartaswa, ya nemi ƴan majalisar da su amince da takardar da ya gabatar domin siyo motoci ga karan kansa, mataimakinsa da matansu. Kuma cikin gaggawa aka amince da hakan ba tare da wata jayayya ba.” A cewarsa

Ya bayyana cewa majilisar tace tun lokacin da gwamnan ya hau mulki a shekarar 2019, da shi da mataimakinsa suna amfani ne da tsaffin motocin da suka gada a wajen gwamnatin da ta gabace su, saboda haka sun cancanci jihar ta siya mu su sabbin motoci. LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu?

Majiyar ta kuma yi bayanin cewa, a takardar da gwamnan ya gabatar, da shi da matarsa za su samu sama da N1.3bn, sannan mataimakinsa da matarsa za su samu N750m domin siyan motocin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...