Daga Abdulrashid B Imam
Wata Kungiyar Kwararru kan abun da ya shafi zuciya dake Turai ESC, ta bayyana sakamakon wani bincike, inda ta gano cewa yin magana a wayar salula na sama da tsawon a kowane mako na da alaƙa da haɗarin hawan jini da kashi 12 cikin ɗari.
Binciken da Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Kiwon Lafiya ta Kudancin Guangzhou na kasar Sin ya rubuta, ya ce yana da kyau a takaita kiran wayar hannu don kiyaye lafiyar zuciya.
Sakamakon binciken da aka buga a cikin Mujallar Zuciya ta Turai – Digital Health, ESC, an buga shi akan Yanar Gizo na ESC a jiya Juma’a.
Bankwana: Ganduje ya yafewa malaman makaranta kudaden gidaje
“Yawan mintunan da mutane ke kashewa suna magana akan wayar hannu na da tasiri ga lafiyar zuciya. Ƙarin mintuna na yin waya na nufin haɗari.
Inganta aikin Hisbah: Ganduje ya yabawa Shekarau Kwankwaso
“Amma idan za a debi shekaru ana yin waya ta amfani da sautin ta ta waje, hakan ba zai yi wani haifar da cutar hawan jini ba
Sai dai Farfesa Qin yaca akwai buƙatar a gudanar da ƙarin nazari don tabbatar da sakamakon binciken nasa.