Daga Maryam Ibrahim Zawaciki
Dr. Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar kano ya bayyana cewa ya yafewa malaman makaranta kudaden gidajen da gwamnatin kano ta gina domin ba da su bashi ga malaman makarantar.
” Bazan manta da ku ba, shi yasa naga bai kamata ace na tafi ban yi muku bankwana ba, don haka ina mai sanar da ku cewa cewa mutane 91 da suka fara biyan kudaden su Inda har suka bada kaso 10 cikin dari cewa na yafe muku sauran kaso chasa’in”. Inji Ganduje

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da rukunin gidajen a garin Ungoggo dake jihar kano.
Yace gwamnatin kano ta gina gidajen ne don Saukakawa malaman makarantar sakamakon irin gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban al’umma.
” Tun da muka zo gwamnati mun yi abubuwa da yawa don inganta rayuwar malaman makaranta, mun yi muku karin girma kuma mun biyaku hakkokin ku, sannan mun baku dama kun karo karatu don cika ƙa’idar koyarwa, mun dai yi muku abubuwa da yawa don haka ko ku zaku manta da ni ni bazan manta da ku ba”. Inji Ganduje
Ganduje ya ce ya sanyawa rukunin gidajen sunan tsohon shugaban kungiyar ƙwadago ta kasa reshen jihar kano wato Kwamarat Kabiru Ado Minjibir Housing Estate, saboda yadda ya baiwa gwamnatin sa hadin kai lokacin da ya rike Shugabancin kungiyar.