Akalla shaguna 150 ne ake zaton gobara ta lalata a kasuwar ƴan Katako da ke garin Zariya a jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na dare lokacin da mutane ke barci.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban masu samar da tsaro na kasuwar, Hamisu Buhari na cewa gobarar ta tashi ne lokacin da hukumar samar da wutan lantarki da KEDCO ta dawo da wuta, inda wani igiyar wutar lantarki ta faɗa kan ɗaya daga cikin shagunan.
Da dumi-dumi: Kwankwaso ya zama mai baiwa gwamnan kano Abba Gida-gida shawara akan Ilimi
Ya ce daga nan ne kuma wutar ta yaɗu zuwa sauran shaguna da ke cikin kasuwar, inda ya ce duk wani kokari na kiran jami’an kahse gobara ya citura.
Hukumar Yan Sanda ta turo sabon kwamishinanta kano
Ya ƙara da cewa gobarar ta ƙona shaguna sama da 150 kurmus da kuma asarar dukiya ta miliyoyin naira.
Da aka tuntuɓi shugaban hukumar ta KEDCO, Abdul Azeez Abdullahi, ya musanta cewa wutar lantarki ce ta jawo tashin gobarar.
A baya-bayan nan dai ana samun tashin gobara a yawancin kasuwa da ke faɗin Najeriya, inda ake asarar dukiya ta miliyoyn naira.