Gidauniyar Amiruljaishi ta tallafawa masu yoyon fitsari a Kano

Date:

Daga Maryam Ibrahim Muhammad

 

An yi kira ga al’ummar Musulmi da su sake rubanya kokarinsu wajen taimakawa mabukata musamman a kwanaki Goma na karshen watan Ramadan.

 

Shugabar Gidauniyar AMIRULJAISHI FOUNDATION Sayyida Saratu Shaikh Nasir kabara, wacce Sayyida Ummawiyya Shaikh Nasir kabara ta wakilta, ta yi wannan kiran ne a lokacin da take ba da gudunmawar sinadaran wanki ga masu fama da lalurar yoyon fitsar dake Kwalli.

Rarara ya Magantu kan korar yan sandan dake bashi kariya

Sayyida Ummawiyya ta bayyana bukatar jama’a da su rika la’akari da irin wadannan majinyata a lokacin da suke ba da tallafin azumin watan Ramadan saboda yanayin da suke ciki wanda ke bukatar yawan wanke-wanke da sauran kayan tsaftacewa.

 

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta gidauniyar Amiruljaishi Bahijja Malam Kabara ta aikowa kadaura24.

 

A cikin jawabinta mataimakin jami’in kula da Hostel din ta yaba da wannan kabakin alkhairi da wanann gidauniya ta kai, Inda tace sun kai kayan a daidai lokacin da ya dace.

 

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Salama ta godewa gidauniyar bisa tallafin da suka basu.

 

Hakazalika Gidauniyar tana raba kayan abinci ga masu karamin karfi har mutane 100 a duk shekara ta hannun ‘ya’yan Shaikh Nasir kabara mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...