Yadda sabon dan majalisar tarayya na Fagge MB Shehu yaki gaisawa da jami’ar INEC

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Sabon Zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai wanda zai wakilci Ƙaramar Hukumar Fagge, Mohammed Bello Shehu ya burge mutane da dama a yau Laraba, inda ya ƙin gaisawa da jami’ar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, yayin karɓar shaidar lashe zaɓen sa.

 

Kadaura24 ta rawaito a yau labaran ne dai INEC ta miƙa wa waɗanda su ka lashe zabukan na cike-gurbi shaidar lashe zabe a Abuja.

Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil

Da aka zo kan Shehu, bayan da jami’ar ta miƙa masa tashi shaidar, sai ta miƙa masa hannu domin taya shi murna, inda shi kuma sai ya ƙi mika mata masa domin yin musabiha.

Falakin Shinkafi ya rabawa Marayu 100 kayan Sallah a Kano

Daga nan ne dai sai Shehu ya dora nasa hannun a kirjin sa ya kuma rusuna domin girmamawa ga jami’ar.

Kadaura24 ta rawaito a musulunce haramun ne namiji ya gaisa da macen da ba maharramarsa ba .

INEC ɗin ta sanar da Shehu, wanda aka fi sani da MB Shehu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike-gurbi da ya gudana a ranar Asabar.

Shehu ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u dubu 19, 024, inda ya doke abokin karawar sa na jam’iyyar LP, Shuaibu Abubakar, wanda ya samu ƙuri’u 12,789, sai kuma ɗan majilasa mai ci, Aminu Suleman Goro, wanda ya zo na uku da ƙuri’u 8,669.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...