Yanzu-Yanzu: An Tsaurara Tsaro Yayin da Jami’an INEC Suka Sake komawa don tattara sakamakon zaɓen gwamnan Adamawa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Jami’an tsaro sun yi wa cibiyar tattara sakamakon zaben jihar Adamawa tsinke, yayin da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke ci gaba tattara sakamakon.

 

Babban sakataren hukumar zabe ta INEC a jihar, Adamu Gujungu, wanda aka ba da umarnin maye gurbin tsohon kwamishinan zabe Hudu Yunusa Ari, shi aka gani a wurin tattara sakamakon zabe.

Da dumi-dumi : INEC ta bayyana Matsayarta kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Ana sa ran kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye zai kasance a wurin tattara sakamakon zaben.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Lahadi ne INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa da aka gudanar a ranar Asabar bayan Hudu Ari ya bayyana Aisha ‘Binani’ ta APC a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna.

Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil

Nan take INEC ta gayyaci Ari zuwa Abuja tare da ayyana sanarwarsa a matsayin maras inganci da kuma zagon kasa ga jami’in tattara sakamakon .

Kafin a dakatar da aikin tattara sakamakon a daren Asabar, an sanar da sakamakon kananan hukumomi 10 .

Da misalin karfe 11 na safiyar Lahadi ne ake sa ran za a fara tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 10 da suka rage, kuma Mele Lamido, jami’in zaben gwamnan Adamawa, bai halarci wajen taron ba, a lokacin da Ari ya bayyana Binani a matsayin wanda ta lashe zaben.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, Lamido ne kadai jami’in da ya dace ya bayyana wanda ya lashe zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...