Da dumi-dumi : INEC ta bayyana Matsayarta kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, bayan ganawar ta da kwamishinoni hukumar na jihohi a Abuja ta zartar da abubuwa guda uku kan zaben gwamnan Adamawa .

 

A sanarwar da hukumar ta fitar a sahihan shafin ta na Facebook, Hukumar zaben ta ce ta ɗauki matsayar har uku akan batun.

 

1. Zata rubuta takarda zuwa ga Sufeto-Janar na ‘yan sanda domin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da yiwuwar gurfanar da Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa, Barr. Hudu Yunusa Ari.

Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil

2. Hukumar ta bukaci sakataren gwamnatin tarayya da ya jawo hankalin hukumar da ke da alhaki domin ladabtarwa ko daukar matakin da ya dace akan kwamishinan hukumar na jihar Adamawa .

Za a fara allurar rigakafin cutar Maleriya a Nigeria

3. Ta Kuma ɗauki matsayar za a ci gaba da tattara sakamakon zaɓen a duk lokacin da jami’in tattara sakamakon ya amince da shi.

Helkwatar Hukumar ta INEC ta ce zata sake bada cikakken bayanin yadda zaman tattaunawar ya kasancewa a sanarwa ta gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...