Daga Fatima Kabir Labaran
Akwai yiwuwar a ranar Asabar mai zuwa za’a yi Sallah Idin karamar Sallar ta bana a Saudiyya da ma galibin kasashen Larabawa.
Ma’aikatar kula da lamuran addini ta kasar, tare da hadin gwiwa da hukumar amfani da fasahar zamani don hango wata ta ƙasar saudiyya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da suka fitar.
Yanzu-yanzu: INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben Adamawa
DW Hausa ta rawaito Sanarwar da hukumomin suka fita ta bayyana cewa zai yi wuya a iya ganin jinjirin watan Shawwal, don haka akwai yiyuwar a cika Azumi talatin a wannan shekarar.
Dama dai ana malaman addinin musulunci suna Fadi n cewa idan ba’a ga watan Shawwal ba , ana cika Azumi ne zuwa 30 sai a yi Sallah.
Kadaura24 ta rawaito idan aka yi azumin 30 a bana kusan Shekaru uku kenan a Jere ana gudanar da Azumi 30 a Nigeria, duk da wasu kasashen a bara Azumi 29 suka yi.