Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kungiyar tallafawa marayun Karaye ta tallafawa iyayen marayu akalla guda 1500 da kayan abinchi domin saukaka musu radadin mawuyacin halin da suke ciki.
Da yake jawabi a wajen taron Shugaban kungiyar Alh. Hamza Abdulmumini Karaye, yace sun fara gudanar da wannan aikin ne tun a Shekarar da ta gabata domin fitar da marayun daga matsananci halin da suke tsintar kawunansu a ciki.
Ramadan: Akwai yiwuwar za a cika Azumi 30 a bana
” Muna zabo iyayen marayun ne don da suke da karamin karfi ne Kuma mu basu dan abun da Allah yasa muka tara a tsakanin mu ‘yan’yan wanann kungiyar don neman yardar Allah “.inji shi
Cutar kansar baki tana kashe yan Najeriya 764 a duk shekara – Gwamnatin Tarayya
Alhaji Hamza Abdulmumini ya kuma yi kira ga mawadata da sauran al’umma da su taimaka wajen bada tasu gudunmawar don taimaka marayun da suke bukata, saboda yin hakan zai magance matsalolin da al’ummar wannan zamanin suke ciki.
Yayin taron da aka gudanar a dakin Cibiyar Addanin Musulunci ta Garin Karaye, wasu daga cikin iyayen marayun da suka amfana da tallafin sun yabawa kungiyar tare da bada tabbacin zasu yi amfani da kayan da aka basu ta hanyar data dace.