Daga Umar Sani Korar Na’isa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Dr. Nasiru Idris kauran Gwandu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi.
Farfesa Yusuf Sa’idu Udus Sokoti ne ya bayyana sakamakon Zaɓen a cibiyar tattara sakamakon ƙarashen zaɓen gwamnan jihar Kebbi.
Yanzu-yanzu: INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben Adamawa
Yace Dr. Nasiru Idris na jam’iyyar APC ya sami kuri’u 409,225, yayin da Gen. Aminu Bande na jam’iyyar PDP ya sami kuri’u 360,940, ” Aminu Idris na jam’iyyar APC shi sami kuri’u mafi rinjaye kuma ya cika dukkanin ka’idoji da suka kamata don haka shi ne ya lashe zaɓen”.