Kotu ta yanke wa wasu barayin shanu 2 daurin shekaru biyar-biyar

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Wata Kotun Majistare da ke Gwagwalada, babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wasu barayi biyu, Buba Bello da Abubakar Umar hukuncin daurin shekaru biyar kowanne su a gidan yari tare da aikin wahala bisa samun su da laifin satar shanu guda 14 da kudinsu ya kai Naira miliyan 2.5.

 

Ƴansanda ne su ka gurfanar da Bello mai shekaru 30 da Umar mai shekaru 26 bisa samun su da laifin hada baki, tsoratarwa, zamba, sata da kuma karbar kudi ta karfi.

 

Alkalin kotun Majistare, Munir Sani ne ya yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin bayan sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi, tare da rokon a yi musu sassauci.

 

Sani ya yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso kan kowane laifi ba tare da zabin biyan tara ba.

 

Ya kuma umurci wadanda aka yankewa hukuncin da su biya diyyar Naira dubu 165,000 ga wadanda suka kai kara.

 

Tun da fari, Lauyan masu shigar da kara, Abdullahi Tanko ne ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 3 ga watan Fabrairu a ofishin ‘yan sanda na Gwagwalada, ta hannun Mista Muhamodu Bello da Usman Dikko, na kauyen Dukpa Gwagwalada, Abuja.

 

Tanko ya ce a ranar 21 ga watan Janairu wadanda aka yanke wa hukuncin da kuma wani Umar, wanda ya tsere, sun hada baki, sun shiga gonar wani Bello (mai kara na farko) inda suka sace shanu 14 da kudinsu ya kai Naira miliyan 2.5.

 

Ya ce daga baya wadanda aka yanke wa hukuncin sun kira shi suka bukaci a ba su N250,000 kafin su sako masa shanun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...