Kisan Ummita: Ba da niyyar kisa na daɓa mata wuƙa ba, in ji ɗan China da ya hallaka budurwarsa a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wani dan kasar China mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47, a yau Alhamis ya tabbatarw wata babbar kotu a Kano cewa ya daɓa wa budurwarsa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani wadda aka fi sani da Ummita wuka.

 

Wanda ake tuhumar, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, na ci gaba da gurfana ne a gaban kotun bisa laifin kisan kai.

DSS ta ce ta gano makarkashiyar kafa gwamnatin rikon kwarya a Nigeria

 

Frank da lauyan masu gabatar da kara ke yi masa tambayoyi, Darakta mai shigar da kara na jihar Kano, DPP, Aisha Mahmoud, ya shaida wa kotun cewa a wannan ranar da ibtila’in ya afku, abubuwa da dama sun faru.

Amurka ta ƙara wa ‘ƴan Najeriya kuɗin neman takardar visa

 

Ya shaida wa kotun cewa ya zo Najeriya ne a 2019 domin yin aiki a matsayin Manajan Kasuwanci da Tallace-tallace a Kamfanin BBY Textile Kano.

 

“Ana biya na Naira miliyan 1.5 duk wata kuma ina yin wasu harkokin daban-daban. A ranar da kaddarar ta afku, Ummukulsum ta tura ni kan gado.

 

“Na caka mata wuka ne ba tare da niyyar kashe ta ba.

 

“Na fita daga dakin ta taga tunda an kulle kofa daga waje ina so in kai Ummukulsum ɗin asibiti amma sai ‘yan sanda suka iso suka kama ni,” in ji Mista Frank.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...