Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jarumin barkwancinan Ali artwork wanda aka fi Madagwal ya yi Martani kan yan kwankwasiyya da suke gwaba masa magana da cewa ba zasu karbe shi ba a cikin tafiyar ba, saboda sanda yana Gandujiyya yaci mutuncin su.
Jarumin ya bayyana hakan ne a sashihin shafin sa na Facebook.
“Ya Kamata Kwankwasawa Ku Yi Min Uzuri Wancen Gidan Da Kuka Ga Na Faɗa A Ciki Jifa Na Aka Yi Amma Yanzu Allah Ya Taimake Ni Na Dawo Hayyacina Don Sai Da Aka Yi Ta Yi Min Sauka Kafin Na Dawo Daidai Amma Kowa Ya San Tun A 2019 Ni Ɗan Amanar Madugu Ne”. Inji Madagwal
Madagwal dai ya dawo tafiyar kwankwasiyya ne bayan da aka bayyana Abba Gida-gida a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar kano wanda akai a ranar asabar 18 ga watan maris na 2023.
Bayan komawarsa ne Yan kwankwasiyya suke ta yi masa kalamai marasa dadi, sakamakon irin kalaman da ya rika fadawa Jagoran su lokacin yana cikin gwamnatin jihar kano ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje.