Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana Umar Namadi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Jigawa.
Jami’in zaben, Farfesa Umar Zaiyan na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi ne ya sanar da sakamakon zaben a jiya Lahadi a Dutse.
Zaiyan ya ce Namadi ya samu kuri’u 618,449 inda ya doke abokin hamayyarsa Mustapha Sule Lamido wanda ya samu kuri’u 368,726.
Ya ce: “Ni Farfesa Umar Zaiyan na tabbatar da cewa Umar Namadi na jam’iyyar APC, bayan ya cika sharuddan doka an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jigawa.”
A cewarsa, mutane miliyan 1.07 aka tantance a zaben na ranar 18 ga watan Maris da kuri’u miliyan 1.05, daga cikin kuri’u miliyan 1.03 da aka kada a zaben.