Daga Kamal Yahaya Zakaria
Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta ta ayyana dan takarar gwamnan jihar kano na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan kammala tattara sakamakon.
“Abba Kabir Yusuf shi ne wanda ya Sami kuri’u mafi yawa Kuma ya cika duk wasu tanade-tanaden doka don haka shi ne ya lashe zaben gwamnan kano”. A cewar Farfesa Ahmad Doko
Yace Abba Kabir Yusuf ba jam’iyyar NNPP ya Sami kuri’u 1,190,602 yayin kuma da Mai biye masa Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ya sami kuri’u 890705.