Daga Isa Ahmad Getso
Babban sifeton yan sanda, Usman Alkali Baba, ya turo CP Ahmad Kontagora, zuwa Kano a matsayin sabon kwamishinan yan sanda da zai jagoranci gudanar da zaben gwamna da na yan majalisar dokoki na jiha.
Wannan ya biyo bayan dakatar da turo CP Feleye Olaleye, da babban sifeton yan sandan ya yi, bayan an turo a makon da ya gabata a kwamishinan yan sandan jihar.
Amma a wata takardar da aka fitar ranar Litinin mai lamba TH.5361/FS/FHQ/ABJ/SUB.6/144, Babban Sufeton yan sandan yace CP Ita Lazarus Uko-Udom zai cigaba da kula da Kano ta Tsakiya, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Ku Karanta: Da dumi-dumi: Bayan hukuncin kotun koli CBN ya Magantu akan amfani da tsofaffin kuɗi
Yayin da sanarwar ta umarci DCP Abdulkadir El-Jamel don kula da kananan hukumomin Albasu, Gaya, Rogo, Takai, Ajingi, Garko, Wudil da Sumaila.
DCP Adamu Ngojin zai kula da kananan hukumomin Rano, Bebeji, Bunkure, Doguwa, Kiru, Kibiya Tudunwada dake Kano ta Kudu.
Ku Karanta: Gobara ta kone Shaguna da dama a Kasuwar Singer dake Kano
IGP din ya kuma ci gaba da rike DCP Abaniwonda Olufemi zuwa Kano ta Arewa, inda ACP Adamu Sambo a matsayin wanda zai dafa masa.
A sabuwar siginar, DCP Auwal Musa zai ci gaba da rike mukaminsa na DC CID, yayin da DCP Aminu Maiwada aka maye gurbinsa da DCP Nuhu Darma a matsayin DC Operations a Rundunar yan sandan Kano.
A yan kwanakinnan dai rundunar yan sandan ta turo kwamishinonin yan sanda akai-akai zuwa jihar Kano, wanda ya janyo korafi da gudanar da zanga-zanga daga magoya bayan jam’iyyar adawa ta NNPP, sakamakon yunkurin turo tsohon babban jami’in tsaron gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje wato CP Balarabe Sule, wanda shi ma aka dakatar da turo shi.