Kano 2023: Zan bayar da ilimi kyauta, da tura dalibai kasashen waje, idan ya zama gwamna – Abba Gida-gida 

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria
 Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Engr.  Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin idan aka zabe shi a matsayin gwamnan kano, zai gyara yanayin da makarantun gwamnati ke ciki don su dace da ka’idojin da ke tabbatar da ingantaccen ilimi da talakawa ke bukata.
 Engr. Abba Kabir, wanda ya yi wannan alkawarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon Rahma Kano, ya nuna damuwarsa kan tabarbarewar harkokin ilimi a Kano, biyo bayan gazawar gwamnati mai ci na samar da tallafin ilimi wanda wani hakki ne na kowane dan kasa.
 Ya ce akwai bukatar Malaman makarantun firamare da sakandire su sami horo na musamman saboda yawan daliban da ake da su a jihar Kano, ga rashin kayan aiki, rashin kwararrun malaman da rashin kwarin gwiwar dalibai da malamai wanda hakan ya kawo kusan durkushewar bangaren ilimi a kano baki daya.
 Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP ya ce farfado da fannin ilimi a Kano, wani shiri ne da ya ta’allaka a cikin tsarin tsarin NNPP wanda ya kunshi samar da kayan aiki na zamani da abinci kyauta da kayan makaranta da kayan karatu da kudin makaranta a matakin firamare da sakandare.
 Hakan na cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben NNPP, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24 a ranar Litinin .
 Sanarwar tace dan takarar gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar a karkashin sa za ta dawo da martabar manyan makarantun da makarantun sakandaren gwamnati. Sannan yayi alkawarin biyawa dalibai kudin WAEC da NECO idan aka zabe shi gwamnan kano.
 Engr. Abba ya ce malaman makarantun gwamnati za su zage damtse ta hanyar biyan su cikakken albashi, horar da su don cika ka’idojin zamani na ba da ingantaccen ilimi wanda zai yi tasiri mai kyau ga yan jihar kano .
 “Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Engr. Abba da tsarin Kwankwasiyya zai jajirce wajen baiwa daliban Kano tallafin karatu na manyan makarantu da digirin digirgir a kasashen waje ba tare da la’akari da zamantakewa da tattalin arzikin iyayensu ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...