Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna a Kano Nasiru Gawuna ya jajantawa waɗanda ibtilain gobara ya shafa a kasuwar singa ta Kano.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a safiyar Litinin din nan an sami gobara wadda ta lashe dukiyoyi Masu tarin yawa a kasuwar Singer dake jihar kano.
Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana alhininsa ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa Hassan Musa Fagge ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
- ” A madadin ni kaina da mataimakina a takarar gwamnan Kano da dukkanin magoya bayan mu , Muna mika Sakon jaje ga waɗanda suka rasa dukiyoyin su yayin wannan iftila’in”. Inji Gawuna
Karanta: Gobara ta kone Shaguna da dama a Kasuwar Singer dake Kano
Sannna ya yabawa hukumar kashe gobara ta jihar Kano bisa ƙoƙarin ganin sun shawo kan lamarin.
Ya kuma yi jaje ga waɗanda gobarar ya shafa ya na mai cewar lamarin abin takaici ne matuƙa.
Gawuna ya yi addu’ar Allah ya Mayar musu da alkhairi ya kuma kare afkuwar hakan a nan gaba.