Daga Maryam Abubakar Tukur
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bada tabbacin gwamnatin jihar a shirye take domin gudanar da zaben gwamna mai zuwa cikin kwanciyar hankali ta hanyar kara wayar da kan jama’a a tsakanin mabiya jam’iyyu.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbar bakuncin tawagar kwamitin zaman lafiya na Kano a gidan gwamnati.
Ya yi nuni da cewa a yanzu lokacin zabe ne akwai bukatar a kula da kyau domin kaucewa shiga mummunan yanayi ta hanyar yin taka tsantsan musamman akan duk wani abu da ya shafi jam’iyyun Siyasa da magoya bayan su.
Gwamnan ya kara da cewa batun zaman lafiya a lokacin zabe ya kunshi abubuwa daban-daban da suka hada da duk masu ruwa da tsaki kamar ‘yan siyasa, jami’an tsaro, jami’an INEC wadanda dukkanin su akwia bukatar su bada tasu gudunmawar domin magance rikice-rikicen zabe.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin zaman lafiya na Kano Dan Amar din Kano Alhaji Aliyu Umar Harazimi, ya ce kwamitin na su na aiki tukuru don ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da luman.
Ya bukaci Gwamna Ganduje da ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar, a matsayin sa na shugaban al’ummar jihar kano.
A jawabinsa tun da farko babban Lauyan Najeriya wanda daya ne daga cikin shugabannin tawagar Abubakar Balarabe Mahmoud SAN, ya bayyana cewa kwamitin ya ga ya zama wajibi ta tattauna da masu ruwa da tsaki daban-daban domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ya bayyana cewa zaben da ya gabata al’amura sun tafi daidai duk da wasu matsaloli da aka samu a wasu wurare, inda ya yi kira ga hukuma da ta gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotun.