Jami’ai a Afrika ta Kudu na ci gaba da ƙoƙarin gano wani zaki da ya ɓalle a wajen Pretoria, babban birnin ƙasar.
An ga zakin kusa da wata hanyar ƙasa mai nisan kilomita 30 daga yammacin birnin.
Arthur Crewe, ma’aikaci a wani kamfanin tsaro ya ce an soma binciken da ake domin gano zakin a ranar Laraba kusa da Hennops Hiking Trail.
Ana amfani da fasahar nan ta drones domin gano dabbar da aka gani lokuta da dama, kamar yadda ya faɗa wa jaridar TimesLive ta Afirka ta Kudu.
Ya shaida wa News24 cewa yana fatan samun tallafin jirgi mai saukar ungulu.
Mista Crewe ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu inda ya ce ba lalle zakin ya yi wa kowa komai ba saboda yana cikin daji ne.
Babu ƙarin bayani kan daga inda zakin ya tsere.
Wani rahoto da ke cewa zakin ya kashe wani jaki ba gaskiya bane kasancewar mota ce ta bige jakin.