Mun cire sama da mutum miliyan 100 daga talauci a Nigeria – Gwamnatin tarayya

Date:

Daga Kamal Umar Kurna

Warning
Warning
Warning
Warning

Warning.

Gwamnatin Tarayya ta ce ta kashe naira biliyan 35.5 kan shirye-shiryen taimakawa al’umma a Jihar Taraba tun lokacin da ta ci mulki.

Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala’i ta Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana haka a Jalingo babban birnin jihar, yayin da take wata tattaunawa da waɗanda suka ci moriyar shirye-shiryen.

Ministar wadda shugabar shirin a jihar Beatrice Kitchina ta wakilta ta ce mutum sama da miliyan 100 sun fita daga cikin matsanancin talauci dalilin wannan shiri, kuma ciki har da matasa da mata.

Ta bayyana jerin wasu shirye-shirye kamar su N-Power da CCT da GEEP ga kuma shirin ciyar da ‘yan makaranta shi ma.

Sakataren shirin ciyar da ‘yan makarantar Idris Goje, yace an yi maganin talauci a ƙasa da wannan shiri, haka kuma ya yi amfani a jihar Taraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...