Daga Aliyu Abdullahi Fagge
Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan kano ta kudu.
Farfesa Ibrahim Barde babban Baturen zaɓen shiyyar Kano ta kudu shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Rano.
Yace kawu Sumaila shi ne ya Sami kuri’u mafi rinjaye Kuma ya cika dukkanin ka’idoji da hukumar zaben ta tanada don haka shi ne ya lashe zaben Sanatan kano ta kudu.
Kawu Sumaila ya samu kuri’u 319,557 yayin da babban abokin takarar sa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na jam’iyyar APC ya sami kuri’u 192,518, wanda hakan ya nuna Kawu Sumaila shi ne ya samu kuri’u mafi rinjaye.