Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana Sanata Barau I. Jibrin na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan Kano ta Arewa .
Farfesa Tijjani Magaji Bamanga wanda shi ne jami’in tattara sakamakon Zaɓen Sanatan Kano shi ne ya bayyana hakan yau lahadi.
Dan takarar na APC ya samu kuri’u 234, 652 wanda hakan ya sa ya samu nasara a kan babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar NNPP, Dr. Baffa Bichi wanda ya samu kuri’u 177, 014.
Kafin bayyana sakamakon Zaɓen, sai da wakilin jam’iyyar NNPP ya bukaci jami’in zaben da ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba saboda zargin da yayi na cewa wadanda suka kada kuri’a sun fi wadanda aka tantance yawa.
Sai dai jami’in zaben ya bayyana masa cewa babu isassun shaidun da zai ai hakan, inda ya bukace shi ya kai rahoton duk wani korafi ga INEC ko kotu.
Ga Sakamakon zaben a ƙasa:
APC – 234, 652
PDP – 12, 751
NNPP – 177, 014
LP – 1, 258