Daga Halima Musa Sabaru
Gamayyar wasu kungiyoyin matasan arewa sun nuna goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party Peter Obi a zaɓen da za a gudanar a gobe Asabar 25 ga watan fabarairun 2023.
“Mun tara wakilan kungiyoyin matasa 56 daga jahohin Arewa 19 a dakin taro na Arewa House Multipurpose Hall, Kaduna, domin mu tattauna da yin magana da murya daya, kuma duk mun Amince zamu Marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party Peter Obi a za a gudanar gobe Asabar”.

Hakan na dauke ne cikin wata takardar bayan taron da gamayyar kungiyoyin suka aikowa kadaura24 mai dauke da sa hannun Amb. John Mathew Karachi Sakatare kungiyoyin da kuma Bilal Tijjani Paki Darakta ayyuka na musamman.

” A madadin manyan kungiyoyi, AREWA YOUTH COUNCIL, AREWA CITIZENS WATCH FOR GOOD GOOD GOVERNANCE, SIR AHMADU YOUTH COUNCIL OF NIGERIA, da dai sauran su, mun amince da takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Mr. Peter Obi Kuma Muna fatan shi ne zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin sabon Shugaban kasar Nigeria”. Inji sanarwar
kungiyoyin sun ce suna kara kira ga daukacin ’yan Arewa da ’yan Najeriya da su kawar da ban-bancin addinin, kabilar ko yanki su mara wa Peter Obi goyon baya don samun nasara a babban zaben da za’a yi gobe. “Mu a matsayinmu na masu zabe ne za muke da alhakin yanke shawarar wanda zai zama shugaban kasan mu ta Najeriya don inganta Rayuwar yan kasa”.
“Dole ne mu fito mu tsaya tsayin daka don muga Peter Obi ya samu nasarar zabe domin muna da yaƙinin zai iya kawo karshen wahalhalu da matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar nan musamman abin da ya haifar da karancin man fetur da cin hanci da rashawa da rashin tsaro da karancin kudi. Don haka muna kira ga daukacin miliyoyin mambobinmu da ke a jahohin Arewa 19 da su fito a ranar 25 ga Fabrairu, 2023 domin kada kuri’unsu”. A cewar sanarwar
Sanarwa ta kuma ce wannan shi ne kudurin da suka dauka a karshen taron da suka kwanaki 2 suna yi, kuma suka ce sun dauki wannan matsaya ne domin hadin kai, da ci gaban Nijeriya.