2023: Ba ni bane halastaccen dan takarar sanatan kano ta tsakiya a NNPP ba – Shekarau

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

Da alama an shiga ruɗani game da takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP kasancewar bayanai na nuna cewar har yanzu sunan Sanatar Malam Ibrahim Shekarau ne a hukumar zaɓe ta INEC.

Wannan na zuwa ne duk da irin ƙokarin da bangaren NNPP din suka yi na ankarar da INEC ɗin tare da rubuta musu takardar cewa sun sauya sunan Malam Shekarau da na Sanata Rufa’i Sani Hanga.

Talla

A tattaunawarsa da BBC, Malam Ibrahim Shekarau ya ce shi da kansa ya rubuta wa INEC cewa a sauya sunansa saboda ya bar jam’iyyar, amma sai ta ce masa lokacin canza sunan ɗan takara ya wuce, sai dai, idan ɗan takara ne ya rasu.

Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil

Ya ce tuni ya bar jam’iyyar NNPP kuma ba ita yake wakilta ba, inda ya ce ko da ya ci zaɓe ba a cikinta yake ba.

Sanata Shekarau ya kuma ce ya kira wanda yake takarar kujerar ta sanata a jam’iyyar NNPP, inda ya ce masa ya dakatar da yakin neman zaɓe saboda ba sunan shi ne a jerin sunayen da hukumar zaɓe ta san da su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...