Daga Maryam Abubakar Tukur
Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da al’ummar jihar Kano cewa, CP Muhammad Yakubu ya kama aiki a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano yayin da CP Mamman Dauda aka tura shi rundunar ‘yan sandan jihar Filato domin Sanya idanu a zaben 2023 .
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a kano
Kiyawa ya kara da cewa, haka kuma CP Ita Lazurus Uko-Udom an tura shi zuwa shiyyar Kano ta Tsakiya, DCP Adamu Isa Ngoji da DCP Abdulkadir El-Jamal an tura su shiyyar Kano ta Kudu sannan DCP Abaniwonda S. Olufemi aka tura shi shiyyar Kano ta Arewa domin lura da babban zaben 2023.
Ya bayyana cewa, rundunar ta yabawa al’ummar jihar Kano bisa addu’o’i, goyon baya, karfafa gwiwa da hadin kai da suke baiwa Rundunar a kowanne lokaci domin kara inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar
“Saboda haka, muna neman hadin kan kowa da kowa, yayin da muka kuduri aniyar tabbatar da sahihin zabe, na gaskiya, tare da yin duk mai yiyuwa don ganin an yi babban zaben 2023 lami lafiya” ya tabbatar.