Daga Rahama Umar Kwaru
Hukumar kidiya ya kasa ya bukaci yan jaridu da su baiwa hukumar hadin kai domin samun nasarar gudanar da kidiyar da zata gudanar a wannan shekara.
Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan hukumar a nan Kano Dr. Isma’il Lawan Sulaiman ne ya bayyana hakan yayin wata bita yini guda da hukumar ta shiryawa yan jaridu a Kano .
Kwamishinan yace yan jaridu yana da gagarumar gudunmawa da zasu baiwa hukumar wajen nan hukumar ta Sami nasarar gudanar da kidayar ta bana .
” Kamar yadda muka shirya muku wannan bitar hakan sauran hukumomin irin namu na jihohin kasar nan sun shiryawa abokan aikin ku irin wannan bitar, Kuma fadakar da ku abubuwan da zamu yi don haka muna bukatar hadin kan ku domin mu Sami nasarar gudanar da kidayar” . Dr. Isma’il Lawan
Yace kidayar bana ta banbanta da wadanda aka taba yi a kasar nan, saboda za a yi ta ne da na’urar zamani, don tafiya dai-dai da zamani da kuma tafiyar da kidayar kasar nan daidai da tanadin majalisar dinkin duniya.
” Yanzu haka mun kusa kammala duk wasu shirye-shiryen gudanar don gudanar da kidiyar bana , kuma wannan bita da muka shirya muku na daga cikin shirye-shiryen da muke yi don ganin an gudanar da kidayar cikin nasara”. Dr. Isma’il Lawan Sulaiman
Dr. Isma’il Lawan ya bukaci yan jaridun dake jihar kano da su taimakawa hukumar wajen wayar da kan al’umma don su fahimci muhimmancin kidayar da alfanun da hakan ke da shi wajen cigaban kasa .