Daga Abdulrashid B Imam
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ce tsarin a kasa a tsare, a raka ba zai yi aiki ba a zaɓen bana.
INEC ta shaida hakan ne a wata tattaunawa da BBC ta yi da jami’arta, a ci gaba da kawo muku bayanai kan muhimmanci abubuwa da ya kamata a sani ko tunatarwa kafin ranar zaɓe.
Hukumar INEC ta ce a yanzu sai dai a ce a kasa a tsare a rumfar zaɓe, saboda komai zai kasance cikin na’ura wanda za a ke aikewa kai-tsaye zuwa cibiyar tattara sakamako.
Hajiya Zainab Aminu Abubakar da ke magana da yawun hukumar ta ce ta yanar gizo za a rinƙa aike sakamakon zaɓen.
BBC ta duba abin da ake sa ran masu kaɗa kuri’a za su yi don ganin an yi zaɓe mai tsabta, cikin lumana da nasara da adalci.
Tanadi katin zaɓe
Duk irin shirin da hukumar zaɓe da sauran hukumomin ƙasar suka yi don gudanar da zaɓe mai inganci, ana ganin tilas su ma masu zaɓen sai sun bayar da ta su gudunmawar ta hanyar gudanar da lamurra cikin kimtsi.
Kuma ko shakka babu, yanzu haka ‘yan Najeriya da dama suna nan cike da zummar fita su kaɗa kuri’unsu a zaɓukan da ke tafe, shi ya sa Hajiya Zainab Aminu Abubakar, ke tunasar da cewa;
“Ana bukatar duk wanda ya yi rajistar zaɓe ya nemo katin zaɓensa, ya kakkabe ya adana. Saboda a ranar zaɓe a fita, a je a kaɗa kuri’a.”
Sannan jami’ar ta ce, da zarar mutane sun kada kuri’arsu, idan sun zaɓi su koma gidajensu, sai su tafi.
Idan kuma sun zaɓi su tsaya a rumfar zaɓe, su duba yadda ake gudanar da zaɓe har a kammala, za su iya tsayawa.
Amma fa komai ta intanet za a yi “da zarar sakamakon ya hau yanar gizo, ba za a iya canza shi ba, ko a lalata shi ko kuma a kawo wani sauyi a sakamakon zaɓen ba”.
A guji karya dokoki
Akwai kuma bukatar masu zaɓe su guji aikata laifukan da za su jefa su cikin matsala, a cewar Barista Bello Galadi, tsohon shugaban reshen ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya, wato NBA, na jihar Zamfara.
“Domin akwai laifuka masu yawa na zaɓe, waɗanda dokoki suka hana aikatawa, kuma aka tanadi hukunci da za a iya yi wa duk wanda ya karya dokokin.
“Kamar laifin da ya shafi sayen kuri’ar mutum ko katin zaɓe na wani.
“Sannan sashe na 53 na kundin dokokin zaɓe na kasa, shi ma ya bayar da dama ga duk wanda kuri’arsa ta dan sami matsala, to yana iya gabatar da ita ga shugaban wannan rumfa ta hukumar zaɓe, domin ya musanya masa wata, ya sake zaɓar wanda ya ke bukata”.
Barista Bello Galadi, ya yi kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan, kuma su jefa kuri’a cikin tsanaki, a yi zaɓe cikin lumana da aminci.
Kowa ya zaɓi wanda yake bukata, ba tare da da an yi husuma ko karya doka ba.
Daukar ƙaddara
Lauyan ya kuma shawarci ‘yan takara da magoya baya na dukkan jam’iyyun siyasa, da su shirya rungumar kaddarar da ke tattare da sakamakon zaɓe tun yanzu.
Duk wani abu da ke kawo tashin hankali ko hayaniya, kamata ya yi su ‘yan takara su shiga gaba, don magance shi.
Bai kamata su bari a yi hayaniya ko buge-buge ko kashe-kashe saboda zaɓe ba, in ji Lauyan.
Barista Bello Galadi ya yi nuni cewa, duk ɗan takarar da ya ke ganin an zalunce shi wajen bayyana sakamakon zaɓe, yana iya zuwa kotun sauraren kararrarkin zaɓe, inda za a duba korafinsa a bi kadin abin.
Idan kuma an gano yana da gaskiya kotu ta kwato ma ka hakkinka, ta ba ka.
Ranakun zaɓuka
A ranar Asabar za a gudanar da zaɓen shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya.
A ranar 11 ga watan gobe na Maris kuma a gudanar da na gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na jihohi.
Ana dai sa ran mutane fiye da miliyan casa’in za su fita don kaɗa kuri’unsu a waɗannan zaɓuka