Kwankwaso zai lashe zaɓe da ratar sama da ƙuri’a miliyan 3 – PCC

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Kwamitin kamfen din takarar shugabancin kasa ta Rabi’u Kwankwaso, ya yi hasashen cewa dan takarar zai kayar da abokan takararsa da tsiran sama da kuri’u miliyan uku a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kwamitin ya bayyana hakan ne a jiya Litinin cikin wata sanarwa da Precious Elekima, Ko’odineta na Kudu-maso-Kudu kuma memba da ya fitar.

Talla

A cewar kwamitin, Rabi’u Kwankwaso zai yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya za su iya zabar shugabanni masu nagarta da kima.

Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil

Kwamitin na Kwankwaso ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin cewa zai narke ya haɗe da na takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Kwamitin ya ce Atiku zai gwammace, “ya ruguje tsarinsa ya shiga tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na Sen. Kwakwanso a wani taron da aka shirya yi a ranar 22 ga Fabrairu, 2023, a otal din Transcorp Hilton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...