Daga Rabi’u Usman
Shehun Borno a jihar Kano Kuma Sarkin kabilar Kanuri Mazauna kano Alhaji Mustapha Lawan (mai kanuri) yayi kira ga yan kabilar kanuri mazauna jihar kano dasu fito su yi zaben shekarar 2023 ba tare da farbar ba don sauke nauyin da kundin tsarin mulki Nigeria ya dora musu .
Kadaura24 ta rawaito Wakilin shehun Borno a jihar kano ya bayyana hakan ne yayin da ya kamata gana da manema labarai kan Zaben shekara ta 2023 dake tafi.
Sarkin ya Umarci dukkannin kabilar Kanuri mazauna kano dasu fito kwansu da kwarkwata su zabi wanda suka ga ya Chanchanta a wajen su ba tare da tashin hankali ko hayaniya ba yayin gudanar da zabukan da muke tunkara na 2023.
Daga nan yayi Addu’ar samun zaman lafiya ga jihar kano da Borno dama kasa baki daya.
A karshe yace ya zama wajibi ga duk Dan Kasa na gari ya fito ya yi zabe sannan ya baiwa Jami’an tsaro hadin kai wajen yin aikin su kamar yanda doka ta tanada.