Da dumi-dumi: INEC ta kammala rabon wasu daga cikin kayan zabe a Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala rabon wasu daga cikin kayayyakin aikin zabe ga kananan hukumomi arba’in da hudu a jihar Kano kwanaki 4 kafin babban zaben 2023.
 Jami’in zaben karamar hukumar Gwarzo Mal. Bello Ismail ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki a ofishin sa dake karamar hukumar Gwarzo ta jihar kano.
Talla
 Malam Bello Ismail ya kara da cewa ofishin zabe na karamar hukumar Gwarzo ya samu sama da kashi casa’in cikin dari na kayan da ba su da muhimmanci a halin yanzu.
Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil
 A sanarwar da jami’in yada labarai na karamar hukumar Gwarzo Rabi’u Khalil ya aikowa kadaura24 yace Malam Isma’il ya kuma kara da cewa an sami wadanda suka chanza wuraren kada kuri’arsa zuwa sabbin rumfunan zabe a da aka samar a Damunawa, karkari, sabon garin Kayyu,unguwar Fulani da wasu garuruwa guda bakwai.
 Da yake jawabi a lokacin taron mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa Gwarzo Alh.Sani Lakwaya ya tabbatar da cewa sun gargadi ‘ya’yan jam’iyyar su kan rashin da’a da tashin hankali a lokacin zabe a karamar hukumar Gwarzo.
 A nasa  jawabi mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP da shugaban jam’iyyar APM na karamar hukumar Gwarzo sun yi kira ga mambobinsu da su gudanar da gudanar da zaben cikin lumana tare da kaucewa daukar makamai a yayin gudanar da zaben 2023 mai zuwa.
 A nasu bangaren jami’in hukumar Civil Defence Muhammad Hassan Usman da wakilin ‘yan sanda reshen Gwarzo Surajo Lawan sun tabbatar da cewa jami’an tsaro a shirye suke domin shawo kan duk wata barazana da ka iya tasowa a lokacin zabe da bayan zabe a karamar hukumar Gwarzo.
 Sai dai sun gargadi mutane da su bi doka da oda a lokacin zabe mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...