Daga Kamal Yahaya Zakaria
Al’ummar jihar kano da magoya bayan jam’iyyar NNPP damasu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP sun yi shirin tarbar jagoran jam’iyyar kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso wanda aka ce zai je Kano a ranar Alhamis 23 ga watan Fabrairu, 2023 domin kammala gangamin yakin neman zabensa a fadin kasar.
Sanata Kwankwaso, ya riga ya kai ziyara jihohi 35, kuma zai Sami kyakyawar tarba ta musamman daga magoya bayansa a Kano karkashin jagorancin dan takarar gwamnan jihar NNPP a 2023, Engr. Abba Kabir Yusuf.
A sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban mai magana da yawun yakin neman zaben Abba Kabir Yusuf ya aikowa kadaura24, yace ana sa ran magoya bayan jam’iyyar NNPP za su hadu a Kwanar Dangora da ke kan hanyar Kano zuwa Zariya da karfe 10:00 na safe domin taro dan takarar.
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP da magoya bayan ta sun shiga zabukan shugaban kasa da na gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na Jiha tare da fatan samun nasarar lashe zaben ganin yadda jam’iyyar ke da farin jini da karbuwar jama’a a fadin jihohin kasar nan 36.