Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce farashin man fetur ya ƙaru da kashi 55 a watan Janairu.
Wannan na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, inda ta ce a watan na Janairu, ‘yan Najeriya sun biya N257.12 a kan kowace lita.
Rahoton ya nuna cewa farashin a watan Janairun 2023 ya ƙaru da kashi 54.52 cikin 100 da kuma karuwar kashi 24.70 a kowane wata.
NBS ta kuma bayyana cewa jihar Imo ce ta fi kowace a sayar da litar man fetur, inda na ta ke a kan N332.14, sai Rivers a kan N327.14 da kuma Akwa-Ibom a kan N319.00.
Ta kuma lura da cewa Sokoto ce jihar da aka fi sayar da man fetur a kasan farashi, inda man fetur ɗin ke a kan N191.43 kan kowace lita, sai Filato a kan N192.14 da kuma Borno a kan N193.91.
‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da biyan sama da N185 kan kowace lita da aka amince da shi a matsayin farashin man fetur sakamakon ƙarancin mai, kamar yadda rahoton hukumar kididdiga ta kasa ya nuna.