Jam’iyyar APC ta sake tsunduma cikin ruɗani da rabuwar kawuna, inda shugabancin jam’iyyar ya bi sahun wasu gwamnonin ƙasar da ke fito-na-fito da manufar daina karɓar tsoffin kuɗi ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Bayan wani taro da Kwamitin Gudanarwar APC na kasa ya gudanar da yammacin jiya Lahadi, jam’iyyar mai mulki ta yi kira ga shugaban ƙasar ya mutunta umarnin Kotun Ƙoli a kan wannan batu.
Taron wanda mahalartansa suka shafe kimanin tsawon sa’a biyar suna tattaunawa a hedikwatar APC ta ƙasa, ya kammala ba tare da wani dogon bayani kan yadda al’amura suka kaya ba.
Sai dai fuskokin gwamnonin APC da suka halarci taron, babu annuri.
Haka zalika, sanarwar bayan taro da shugaban APC na ƙasa ya karanta bayan fitowarsu, taƙaitacciya ce.
Wannan kuwa na zuwa ne adaidai lokacin da yake kwanaki kalilan a gudanar da babban zaɓe. Sannan al’umma na kokawa da yanayi matsin rayuwa da batun sauya kudi ya jefa su.
Batutuwan da taron ya tattauna
Jam’iyyar APC dai ta goyi bayan matsayin gwamnoninta a kan shugaban ƙasa game da dambarwar canjin kuɗin.
Shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya ce sun lura da cewar sabon tsarin canjin takardun kuɗin da gwamantin kasar suka kawo, ya jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin hali.
Sannan suna kira ga gwamnan Bankin Najeriya wato CBN da ministan shari’ah na tarayya, su girmama umarnin da kotun ƙoli ta bayar tun farkon zamanta na a dakata har sai ta yanke hukunci.
Sannan kuma Shugaban APCn na ƙasa, ya ce shugabancin jam’iyya da gwamnonin sun cimma matsaya, a kan Shugaba Buhari ya sa baki game da halin da ake ciki.
Cikin mahalarta taron na yammacin jiya Lahadi, an ga fuskar ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar wato Bola Ahmad Tinubu a ofishin jam’iyyar.
Kimanin gwamnoni 10 da mataimakan gwamna 2 ne suka halarci taron, da shugaban jam’iyyar ta APC mai mulkin ƙasar ya kira, sai dai duk sun ƙi cewa komai kan abin da suka cimma