Gwamnan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga jama’ar jihar da su kwantar da hankulansu kan fusatar da suka yi dangane da wahalhalun ƙarancin kuɗi da ake fuskanta a ƙasar.
Gwamnan ya yi wannan kira ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke Marina, kan matsalar da ake ciki ta sauyin kuɗi a ƙasar.

Sanwo-Olu ya umarci mazauna jihar da su kauce wa duk wani tashin hankali, da zanga-zanga da ƙone-ƙone yana mai cewa hakan ba zai kawo mafita ga matsala ko wahalhalun da ake ciki ba

Ya ce “Ina mai jinjina a gare ku mutanen Legas dangane da haƙuri da juriya da kuka nuna a cikin wannan hali da ake ciki na tsaka-mai-wuya”.
“yan uwana al’ummar Legas, ina kira da tattausar murya a gare ku, a matsayina na gwamnanku, dan Allah ku kwantar da hankula a wannan lokaci, ku guji duk wani abu da zai tayar da hankali da zanga-zanga da kuma ƙone-ƙonea faɗin jiharmu”, in ji gamnan.
“Duk da wahalhalun da kowa ke ciki, tashin hankali ba zai zame mana mafita ba, duka mun sani cewa akwai mutanen da ke son yin amfani da tashe-tashen hankulan ta hanyar yin kalaman da ke tunzura jama’a”
”Kuma duk suna yin wannan ne da nufin hana ku damar kaɗa ƙuri’unku a zaɓen shugaban ƙasa, ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki, dan haka kada ku ba su dama su cimma manufarsu,”in ji Sanwo-Olu.
gwamnan ya ci gaba da cewa ba adalci ba ne kai hari kan dukiyoyin gwamnati da na al’umma.
A ranar Juma’a ne dai aka samu rahotonnin da ke cewa wasu fusatatun matasa sun toshe wasu titunan birnin Legas tare da ƙona tayoyi, sakamakon fusatar da suka yi kan ƙarancin takardun naira a ƙasar.