Chanjin kudi: Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargaɗi waɗanda su ke kalaman tunzura jama’a

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargaɗi ɗai-ɗaikun ‘yan Nigeria da ƙungiyoyi kan yin kalaman da za su iya tunzura jama’a ko tayar da ruɗani a ƙasar.

Gargaɗin na zuwa ne bayan da ake ta samun rahotonnin tashe-tashen hankula a wasu sassan ƙasar sakamakon matsalar ƙarancin takardun sabbin kuɗin ƙasar.

Talla

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun jami’inta na hulda da jama’a Olumuyiwa Adejobi, rundunar ta ce kiran ya zama wajibi yayin ya rundunar ke samun bayanai game da yadda wasu ke mayar da martani tare da furta kalaman da za su iya janyo tashin hankali a ƙasar.

Talla daukar nauyi Hon. Surajo Umar Wudil

Sanarwar ta ce mutanen kan yi kalaman – da za su iya tunzura jama’a domin aikata wasu abubuwan da suka saɓa wa doka – domin cimma wata manufarsu.

A dan haka ne rundunar ke kira ga ‘yan ƙasar da su kwantar da hankulansu, su kuma rugumi zaman lafiya a yayin da gwamnati tarayya ta tabbatar da cewa tana ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalar ƙarancin kudi da na man fetur tare da daidaita al’amura.

Haka kuma sanarwar ta yi kira ga ‘yan ƙasar da su kauce wa duk wani abu da zai tayar da ruɗani da lalata dukikyoyin gwamnati da duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaɓen ƙasar da ke tafe.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana aiki da sauran hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri domin tabbatar da zaman lafiya, don gudanar da harkoki cikin kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...