Da dumi-dumi: CBN ya baiwa Bankuna umarnin cigaba da karɓar tsofaffin kudi

Date:

Babban Bankin Najeriya ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin naira 1,000 da 500 waɗanda yawansu bai zarta N500,000 ba.

Bankin na CBN ya bayyana haka ne a yau Juma’a, bayan koke-koken da ake ta samu a faɗin ƙasar kan wahalar da al’umma ke fuskanta wajen samun sababbin kuɗin.
Talla
Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya tabbatar wa BBC da wannan bayani.
Rahotanni daga wasu jihohin sun bayyana cewa an gudanar da zanga-zanga kan ƙarancin sababbin kuɗin.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
An buƙaci jama’a su kai tsofaffin takardun kuɗinsu zuwa bankuna domin a musanya musu su da kwatankwacin kuɗin amma sababbi, sai dai tun gabanin wannan lokacin babban bankin Najeriya ya yi hani ga ‘yan Najeriya su riƙa cirar kuɗin da ya zarce naira 100,000 zuwa naira 500,000 a kowane mako ga kowane ɗan ƙasar ko ga kamfanoni.
A ranar Alhamis ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga al’ummar ƙasar, inda ya bayyana tsawaita amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N200.
Sai dai duk da hakan wasu jihohin sun buƙaci al’umma su ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗaɗen na naira 1,000 da 500 da kuma 200.
Dama dai kotun ƙolin ƙasar ta ta buƙaci a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har sai lokacin da ta yanke hukunci bayan ƙarar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka shigara a gabanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...