Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da ikirarin cewa gwamnatin tarayya ko babban bankin Najeriya CBN sun ki amincewa da ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 duk da hukuncin kotun koli.
Zamfara, Kaduna da Kogi sun garzaya kotun kolin Najeriya domin neman agaji a madadin al’umomim su domin kalubalantar wa’adin da babban bankin kasar CBN ya kakaba na rufe karbar tsofaffin takardun kudin naira a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kotun koli, a hukuncin da ta yanke a ranar 8 ga Fabrairu, ta umurci dukkan bangarorin da kada su ɗauki wani mataki tare da soke wa’adin 10 ga watan Fabrairu 10, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da aka dage sauraron ta zuwa ranar 15 ga Fabrairu, 2023.

Sai dai kuma cibiyoyin hada-hadar kudi da su ka hada da bankuna da gidajen mai da manyan kantuna da sauran ‘yan kasuwa na ci gaba da kin karɓar tsoffin takardun Naira duk da hukuncin da kotun koli ta yanke.
An ruwaito cewa wasu bankunan sun dogara ne da cewa CBN ya aika musu da umarni a wata takarda.
An kuma ambato gwamnan babban bankin na CBN a wani taro da jami’an diflomasiyya a jiya Talata a Abuja yana cewa daga ranar 10 ga Febrairu tsofaffin takardun kudi za su daina aiki.
Sai dai kuma Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, a daren ranar Talata a wata sanarwa, ya ce:
“Muna so mu bayyana cewa ba gaskiya ba ne gwamnatin tarayya ko babban bankin Najeriya, CBN sun dauki mataki kan halascin kudade za su ci gaba da aiki duba da yadda shari’ar ta ke gaban kotun koli.
“Za a sanar da matsayar gwamnati da na CBN bayan an yanke hukuncin gobe.”