Daga Kamal Yahaya Zakaria
Babban Bankin Najeriya ya samar da wata hanyar da masu tsofaffin takardun kuɗi a Najeriya ka iya shigar da kudin asusun ajiyarsu na banki.
Sai dai wannan tsarin na gajeren lokaci ne, domin zai kawo karshe ne a ranar 17 ga watan Fabrairu.

Ga yadda za a iya shigar da takardun kudin hannu CBN:

Da farko sai ku bude wani shafin intanet na bankin na CBN a cika wani fom, inda daga nan za a ba ka wata lamba ta musamman wadda za ka rubuta kuma ka tafi da kudinka zuwa reshen babban bankin da ke kusa da ku. Amma kana iya cika fom din a harabar babban bankin.
Jami’an tsaro za su tantance asusun da za a zuba kudaden.
Idan akwai wata matsala, bankin zai mayar wa mai takardun kudin dukkan kudaden da ya kai bankin na CBN.
Shigar da kudin na iya daukar mako hudu kafin a kammala.
Akwai kuma wani sharadin na hani ga wani mutum na daban ya kai kudin da ba nashi ba bankin domin a adana su. Wanda ya mallaki kudin ne kawai ke da damar shigar da su da kansa.
Abubuwan da ake bukata su ne: lambar nan da aka samo daga fom din rajista da asusun ajiya da ba shi da wata matsala da lambar BVN ta masu asusun ajiya a Najeriya da kuma katin shaida na gwamnatin tarayyar kasar.