Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen soke lasisin gudanar da harkokin kasuwanci na manyan ‘yan kasuwa ko kuma daukar mataki kan duk wanda ya ki karban tsofaffin kuɗi idan an zo sayan kayansu.
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ne ya yi gargadin a wata
Talla
sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya ce har yanzu doka bata hana karbar tsofaffin kudi ba.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Ya ce kotun koli ta jaddada hukuncin wucin gadi da ta yi kan batun tsofaffin takardun kudin, Inda ta bada umarnin a ci gaba da yin amfani da su tsofaffin kudin tare da Sabbin har sai ta yanke hukunci akai.
Gwamnan yace gwamnati ta Sami labarin cewa wasu ‘yan kasuwa kamar manyan kantuna, kantuna, bankuna, gidajen cin abinci, otal-otal, ‘yan kasuwa a kasuwanni, gidajen mai, wuraren ajiye motoci, da dai sauransu, suna da kin karɓar tsohon kudin wanda kuma hakan ba dai-dai .
Ganduje ya kuma kara da cewa rashin karbuwar kudin da wasu marasa kishi suke yi, na dagula al’amura da dama.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na yau da kullum tare da kai rahoton duk wanda ya ki karban tsohuwar takardar naira zuwa ga hukuma mafi kusa domin daukar mataki.