Chanjin kudi: Za mu mutunta hukuncin kotun koli – Gwamnatin tarayya

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta sa dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1,000 a yau 10 ga watan Fabrairu.

A ranar Laraba ne dai kotun ta bayar da umarnin inda ta ce a dakata da amfani da wa’adin har zuwa ranar 15 ga watan na Fabrairu lokacin da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zmfara suka shigar suna kalubalantar wa’adin.

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Najeriyar, Abubakar Malami, ne ya ce gwamnatin za ta bi umarnin a yayin wata hira da tashar talabijin ta Arise TV, a jiya Alhamis.

Sai dai ministan ya ce yana fatan idan aka koma sauraren shari’ar Kotun Kolin za ta soke wannan umarni, wato ta bar Babban bakin ya aiwatar da tsarinsa na sanya wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudin da bankin ya sauya.

Talla

Malami ya kara da cewa kasancewar Babban Bankin wanda kusa ne a shari’ar, wanda kuma ba a sanya shi ba a cikin karar da gwamnonin suka shigar, hakan ya sa a Kotun Kolin ba ta da hurumin yanke hukunci a kan batun tun ma da farko a cewarsa.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Amma kuma ya ce gwamnati ta yanke shawarar bin umarnin Kotun Kolin ne domin mutunta doka da oda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...